Kadan Daga Cikin Falalolin Azumin Watan Ramadaan

Kadan Daga Cikin Falalolin Azumin Watan Ramadaan

Kadan Daga Cikin Falalolin Azumin Watan Ramadan.

Hakika, Azumin watan Ramadan yana da lada da falala mai girma, kuma yin ibada a cikinsa tana da falala mai yawa wacce tafi ta sauran watanni.

Hadisai da yawa sun fadi falalar Azumin watan Ramadan. Daga cikin Hadisan akwai:

قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: “إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ وَغُلِقَتْ أَبْوَابُ الْنِيرَانِ وَصُفِّدَتِ الشَّيَاطِينَ”. (رواه البخارى).

Ma’ana: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Idan watan Azumin Ramadan ya zo, ana bude kofofin Aljannah, kuma ana rufe kofofin wuta, kuma ana daure shaidanu”. (Bukhari ne ya ruwaito).

عَنْ أَبِى سَعِيدِ الْخُدْرِى رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: “مَا مِنْ عَبْدٍ يَصُومُ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللهِ إِلاَّ بَاعَدَ اللهُ بِذَلِكَ عَنِ النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا”. (رواه البخارى ومسلم).

Ma’ana: An karbo daga Abu Sa’idil Khudri (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Babu wani bawa da zai azumci rana daya saboda Allah, face sai Allah ya nisanta fuskarsa ga barin wuta tsawon shekara saba’in”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).

عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: “مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنبِهِ”. (رواه أحمد).

Ma’ana: An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abinda ya gabatar daga zunubinsa”. (Ahmad ne ya ruwaito).

Hakika, Allah (Madaukakin Sarki) ya yi alkawari gwaggwaba, sakamako ga wanda ya azumci watan Ramadan.

Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk aikin alherin da dan adam ya yi Allah yana ninka masa lada goma har zuwa dari bakwai”, Allah (S.W.T) yana cewa: “Sai dai Azumi, shi nawa ne, ni ake yi wa, kuma ni zan bada sakamakon yin sa. Domin mai Azumi yana da farin ciki guda biyu, farin cikin farko lokacin da zai yi buda baki, na biyu kuma lokacin da zai gamu da Ubangijinsa, hakika, warin bakin mai Azumi yafi turaren almiski kamshi a wajen Allah”. (Muslim ne ya ruwaito).

Allah ya karbi ibadunmu. Amin.

Abdurrahman Abubakar Sada.
28/Sha’aban/1438.
25/May/2017.

® www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.