Kadan Daga Cikin Munanan Dabiun Mutanen Arewacin Nigeria Abun Ayi Kuka

arewa

Kadan Daga Cikin Munanan Dabiun Mutanen Arewacin Nigeria Abun Ayi Kuka

1- A Nigeria ne (Arewa) zakayi alkhairi 99
amma ayi shiru ayi tsit babu mai yi maka
adduar alkhairi da karfafarka akai amma daga
ranar da kayi kuskure daya tak za kaga anyi
caa akan ka kamar a cinye ka.

2- A Nigeria ne (Arewa) za kaga mutum zai
sake maka fuska da dariya amma a zuciyar sa
haushin ka yake ji kamar ya kashe ka.

3- A Nigeria ne(Arewa) za kaga mutum yana
bada labari a kanka yana hakikan cewa akan
wani abu akan ka alhali bai taba ganin ka ba
ko kuma bai taba wata hulda da kai ba kawai
labari shima yaji akan ka.

4- A Nigeria ne (Arewa) duk mai kudi barawo
ne azzalumi ne, amma duk talaka marar ko
sisi bawan Allah ne salihi mutumin kirki.

5- A Nigeria ne(Arewa) kowa malami ne mai
bada fatawa ne.

6- A Nigeria ne(Arewa) Duk malami talaka
shine malamin Allah, amma malami mai rufin
asiri ba malamin Allah bane malamin Gomnati
ne mai ci da Addini ne.

7- A Nigeria ne (Arewa) ba zaka taba jin an
fadi alkhairin Shugaba ba sai bayan ya mutu.

8- A Nigeria ne (Arewa) Zaka ga Limami na
jin haushin mamu, mamu na jin haushin
Liman.

9- A Nigeria ne (Arewa) za kaga talaka yana
tsine wa Shugaban sa wai saboda zalunci
amma da Shugaban ya bashi kudi ya rabawa
yan uwan sa talakawa sai ya cinye ya danne
ya hana su.

10- A Nigeria ne (Arewa) masoyinka shine
adali amma abokin adawar ka kuwa duk kirkin
sa mugu ne azzalumi ne.

11- A Nigeria ne (Arewa) Zaka ga mutum yana
da tarin bukatu sai ya kwana yana barci ya
kasa tashi ya fadawa Allah cikin dare amma
da safe sai ya je ya fadawa mutum dan uwan
sa damuwar sa.

12- A Nigeria ne (Arewa) zaka taimaki mutum
daga Allah ya daga shi to yanzu bashi da
babban abokin ga ba sai kai.
13- A Nigeria ne (Arewa) kyakkyawan zato
yayi karanci amma mummuna kam hmmm sai
abin da ya karu.

14- A Nigeria ne (Arewa) yau mutum har ya
rasa Wanda zai dauka a matsayin Amini ko
masoyi babban aboki saboda ba ka da tabbas
akan sirrinka.

15- A Nigeria ne (Arewa) mutum zai ga kayi
kuskure ya kasa maka fada ko nasiha amma
sai ya fara ya madidi da kai wai kuma abokin
ka ne.

16- A Nigeria ne (Arewa) duk lokacin da ka
yabi wani Shugaba ko wani mai mulki shi
kenan zaka Ji Ana Kiranka Da Dan maula.
Subhanallah.

Domin Haka Wallahi Mutanen Arewa Muji Tsoron ALLAH Mu Gyara Halayen Mu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.