Kamfanin Google Ya Kirkiro Sabuwar Man Hajar Gani Da Ido Video Chat

Kamfanin Google ya ƙirƙiro wata manhajar hira ta bidiyo mai suna Dou da za ta yi gogayya da FaceTime da Skype da kuma Massenger.

Manhajar dai ba ta da banbanci da sauran manhajojin hira ta bidiyo, sai dai ta Google din na bai wa masu amfani da ita damar sanin wanda ya ke kira, ta yadda hakan zai taimaka wa mutum wajen yanke shawarar zai amsa kiran ko kuma a’a.

Kamfanin ya ce ya yi wa tasa manhajar lakani da “ƙwanƙwasa”.

Tun watan Mayu aka bayyana ƙirƙirar manhajar, kuma a yanzu an fitar da ita kyauta ga masu amfani da wayoyin Android da kuma iPhone.

Kamar dai yadda manhajar FaceTime ke aiki, Dou na bukatar lambar mutum ne kawai.

Ana zuga manhajar Duo da cewa ita ce mafi sauki, mafi dogaro ta fuskar ganin ‘yan uwa da abokan arziki tar a lokacin da ka ke magana da su.

Nan da ‘yan kwanaki kadan za a tura manhaja zuwa sassan duniya.

Manhajar ta Dou na daya daga cikin manhajoji biyu na wayar hannu da kamfanin Google ya yi shirin samarwa a cikin ‘yan watanni masu zuwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.