Kareena Kafur Bata Karbi Addinin Musulunci Ba

Kareena Kafur

Kareena Kafur Bata Karbi Addinin Musulunci Ba. Har yanzu tana bin Addinin Hindu ne.

Daga Muhammad Muhammad Freedom Radio Kaduna

Abin takaici shine har kullum wani ya zauna ya kirkiro wani labari na kanzon kurege sai ya nufo al’ummar mu da dashi ko dai saboda son zuciya ko kuma sai ya shigo da wani wanda baya kaunar mu da addininmu cikin fadar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), abin takaici kodai da sunan malamta ko kuma kawai dan farfaganda, maimakon mu fadada bincike, a’a sai mu bi labarin da amin! Ko kuma mu fara kabbara….! bayan addininmu shi kadai ne ba ya karbar komai sai da hujja.

Kalallahu kala rasul…. Kuma an umarce mu da tambayar wadanda suka sani…
Hakan ta sa na yi bincike mai tsanani akan wannan labarin domin fidda jaki daga duma! Kuma na gano karya ne jita-jitar da ake ta yadawa akan wai Kareena ta Musulunta a kafafen yada labarai na zamani.

Da farko dai wannan hoton na Kareena kapoor sanye da jan mayafi ta dauke shi ne a shekara ta 2013 a lokacin da ta kai ziyara garin Amristar (wato mahaifar Tsohon Jarumi Rajesh Khanna) a Punjab dake kasar ta India, inda ta zabi ta kai ziyara wani wurin bautar gumaka da ake kira ‘GOLDEN TEMPLE’ domin neman albarka da kuma yin addu’o’i na neman sa’a akan samun nasara fina-finanta musammam ma fim din da ta yi a shekarar mai suna ‘GORE TERE PYAAR MEIN’ wanda aka saki a ranar 22 ga watan Nuwamba 2013 tare da matashin jarumi Imran Khan. Inda ta samu tarya ta musammam daga dubbannin masoyanta a yankin na Punjabi.

Kada ku mance suma masu bin addinin na Hindu matansu na yin lullubi a gurin bautar Gumaka.

Kareena Kapoor ta ce ita ‘yar addinin Hindu ce kuma ta kara da cewar ba ta fahimtar duk wani abu na ibada a addinin da addu’o’i sai dai tana halartar duk wani buki na ibada da sauransu na addinin.

A gefe guda kafin ta auri jarumi Saif Ali Khan wanda shima yake ikirarin Musulmi ne, ya ce shi tsaka-tsakin Musulmi ne. Makusantar Jarumar sun yi tunani za ta sauya addininta amma jarumin ya ce babu bukatar Kareena ta musulunta kowa ya yi addininsa.

Haka zalika wata cibiyar Malamai ta India mai suna Darul Uloom Deoband sun fitar da wata fatawa kafin auren inda suka ce wannnan aure haramun ne in har Kareena ‘yar Hindu ce! Shari’ah ba ta yarda da zamansu a matsayin ma’aurata ba koda kuwa sun yi auren a Kotu da kuma takardar sheda.

Saboda haka ga dukkan mai neman karin bayani ka duba Jaridar Indian Times ta kafar internet, ko kuma ka shiga sashin bincike na Google ka rubuta ‘Kareena Kapoor visits to Golden Temple at Amristar’ za ka ga karin bayani da kuma hotunan da ake ta yadawa akan cewar ta musulunta.

Dadin dadawa za ka iya duba hollowverse.com a nan ne za ka samu karin bayani ba wai akan Kareena ba kawai duk wasu fitattun jarumai da mawaka za ka samu cikakkun bayanansu akan addinansu da akidarsu da kuma siyasarsu, domin ana dauko duk bayanan da suka fada da bakinsu ne a rubuta babu karya akan addinansu da akidarsu da sauransu.

Ina fata ‘yan uwa na musulmai sun gamsu da wannan takaitaccen binciken da muka yi, addinin musulunci rabo ne sai wanda Allah ya baiwa ba wanda kake so ba ko wanda nake so. Allahu A’alam.

Muhammad Muhammad Freedom Radio Kaduna.
08029696960 email:ammawhite2003@yahoo.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.