Karin Hadisai Guda 14 Masu Bushara Da Gidan Aljannah

Karin Hadisai Guda 14 Masu Bushara Da Gidan Aljannah

HADISI NA ASHIRIN

Sallar da Allah ya fi so itace sallar asuba ta ranar jumaa a cikin jami, kuma duk wanda ke abin da Allah ke so to Allah zai so shi, idan kuma Allah Ya so shi

HADISI NA ASHIRIN DA DAYA

Wanda ya ce Subhanallahil azim Wabihamdihi, zaa dasa masa wata bishiya a cikin gidan Aljanna wadda zai ginda tsinkar alkhairin ta.

HADISI NA ASHIRIN DA BIYU

Manzon Allah ya wanda ya ce, duk wanda ya karanta Subhanakallahumma Wabihamdika Ash-shadu Allah Ilaha Illah anta astagfiruka waatubu ilaika, a wajen jira ko inda ake shiririta ko shirme bayan sun gama kamun su watse ya karanta wannan zai zame masa kaffara bisa ga kura kuran da ya tafka a wurin.

HADISI NA ASHIRIN DA UKU

Manzon Allah (S.A.W) ya ce Hakika fadar Subhanallahi, Walhamdulillahi, Walaila ha Illallahu, Wallahu Akbar, tana girgijewa mutum zunubai kamar yanda bishiya take girgije ganyen da yake zubuwa a kasa. Don haka mai makon mutum ya zauna yana hira to ya yi ta fadar wannan don Allah ya girgije masa zunubain sa.

HADISI NA ASHIRIN DA HUDU

Manzon Allah (S.A.W) ya ce idan dayan ku ya gajiye bazai iya tarawa kansa lada dubu ba to yayi Subhanallahi sau dari sai a rubuta masa lada dubu ko a kankare masa laifuffuka guda dubu.

HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR

Manzon Allah (S.A.W) ya ce hakika Allah ya zabi wasu kalmomi uku wanda ya nace musu to zai samu alkhairin duniya da lahira sune (Subhanallah, Walhamdulillah,Wallahu Akbar. Wanda ya ce Subhanallah zaa bashi lada 20 a kankare masa zunubi 20 Wanda ya ce Alhamdulillah zaa bashi lada 30 a kankare masa zunubi 30 wanda Allahu Akbar zaa bashi lada 20 a kankare masa zunubi 20.

HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA

Manzon Allah (S.A.W) ya ce Bana gaya maka wani abu wanda ya fi haka alkhairi? Kace Subhanallah, Walhamdulillah,Walailaha Illallah, Wallahu Akbar, zaa dasa maka bishiya a cikin gidan Aljanna da kowace kalma da ka fada.
HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI
Manzon Allah (S.A.W) ya ce Wanda ya yi ruwa da kudi bai ba dasu sadaka ba kuma ya yi rowa da dare bai tashi yayi tsayuwar dare ba, to ya lazimci wannan kalma sai ta tsaya masa a matsayin sadakar da bai yi ba da tsayuwar dare da ya kasa bai yi ba Subhanallahi Wabihamdihi ya yi ta fadar wannan sai ya zamu a bakacen kudin da bai bayar ba a bakacen daren da bai yi tsayuwa a cikin sa ba.

HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI

Manzon Allah ya ce wanda zai shiga kasuwa sai ya ce Lailaha illallahu wahdahu lasharikalahu, Lahul mulku, walahul Hamdu, Yuhyi wayumitu, wahuwa hayyulla ya mutu biyadihil khairu wahuwa ala kullhi shaiin kadir. Allah zai rubuta masa lada million daya ya goge masa zunubi million daya zaa daukaka darajar sa million daya sannan zaa gina masa gida a cikin gidan Aljanna.

HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS

Manzon Allah ya ce bana gaya maka abin da ya fi ambaton Allah ka da daddare da rana ba?, to kace Alhamdulillahi Adadama khalaka, Alhamdulillahi mila ma khalaka, Alhamdulillahi adada mafissamawati wama filardhi Alhamdulillahi adada ma aksa kitabuk, Walhamdulillahiala ma akhsa kitabuk, Walhamdulillahiadada kulli shaiin, Walhamdulillahiminha kulli shaiin, kuma ka ce Subhanallahi Adada ma halaka, Subhanallahi mila ma halaka, Adada mafissamawati Wama filardi, Subhanallahi ala ma ahsa kitabuk, Subhanallahi adada kulli shaiin, Subhanallahi minha kullhi shaiin, Subhanallahi wanda ya fadi wannan wato yafi kowane irin ambaton Allah da zakayi fadin duniyar nan Inji Manzon Allah.

HADISI NA ASHIRIN DA TARA

Manzon Allah (S.A.W) ya ce wanda ya min salati kafa 10 lokacin da ya wayi gari, ya yimin salati kafa 10 lokacin da ya yammatu, cetona zai riskeshi ranar Alkiyama.

HADISI NA TALATIN

Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam Ya ce wanda ya ce radhitu billahi rabban Wabil Islamidinan Wabi Muhammadin Nabiyan, aljanna ta tabbata a gareshi, ba wai zata tabbata ba tariga ta tabbatar masa don haka muyi ta fadar wannan kalma don Aljanna ta tabbata a garemu.

HADISI NA TALATIN DA DAYA

Mazon tsira ya na cewa wanda ya yiwa dan Uwansa kyakkyawar Adua batare da dan Uwan nasa ya sani ba Ya ce Allah ga dan Uwana wane yana da bukata iri kaza ka biya masa, ko yana cikin balai ka yaye masa ko yana cikin wata fitina ko damuwa ka dauke masa, ba tare da shi wancan dan uwan yasan kayi masa adua ba koma baka gaya masa ba. Malaika ya na nan kusa da kai sai ya ce amin walaka, kai ma Allah ya baka irin kwatan kwacin abin da ka roka wa dan uwanka. Kunga jamaa mu rinka rokawa yan uwan mu adua mai kyau saboda muma malaiku suyi mana adua mai kyau.

HADISI NA TALATIN DA BIYU

Manzon Allah ya ce wanda ya kare mutun cin dan uwansa baya nan (maana ana kokarin tuzarta dan uwanka baya nan sai kayi kakagida ka kare masa mutuncin sa) to ya zama hakke ne ga Allah ya yanta ka daga wuta.

HADISI NA TALATIN DA UKU

Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam ya ce wanda ya dauke abunda zai cutar da mutane a kan hanya to hakika Allah zai rubuta masa cikacciyar lada, wanda kuma Allah ya rubutawa cikakkiyar lada Allah kozai shigar dashi a Aljanna .

Leave A Reply

Your email address will not be published.