Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 2 Masu Sace Mutane Hukuncin Kisa

Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 2 Masu Sace Mutane Hukuncin Kisa

Babbar kotun shari’a da birnin Makurdi na jihar Benue, ta yanke wa wasu maza 2 wadanda ake zargin masu sace mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkalin kotun Aondover Kakaan, ya yanke hukuncin ne bisa shaidu da hujojin da su ka tabbatar cewa mutanen ne su ka kashe limamin darikar cocin Katolika da ke karamar hukumar Otukpo Alexandra Adeyi.

Wadanda hukuncin ya shafa kuwa sun hada da wani Suleiman Goma da kuma Haruna Idi.

Alkalin kotun ya ce, Bisa shaidun da aka gabatar a gaban kotu, ya tabbata cewa Suleiman Goma da Haruna Idi sun kashe limamin ne da taimakon wani Saidu Abdullahi da Aliyu Garba wadanda tuni su sun tsere ba a san inda su ke ba.

Ya ce Hujjoji sun nuna cewa, an biya Naira miliyan 1 da dubu 500, amma bayan sun karbi kudin sai su ka kashe limamin sannan su ka jefar da gawar sa a dajin.

Source: AL’UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.