Kwamandojin Boko Haram Da Aka Saki Sun Fitar Da Sabon Faifan Video Gashi Ku Kalla

SAKAMAKON FARKO NA MUSAYEN ‘YAN MATAN CHIBOK DA KWAMANDOJIN BOKO HARAM

A yammacin jiya Juma’a ‘yan ta’addan Boko Haram da sukeyiwa kungiyar aikin hada video karkashin jagorancin #Abu_Bakr_Sulaiman suke daurawa a shafin youtube sun fitar da sabbin faifan video guda biyu sai suka daura a youtube

Video na farko da suka fitar za’a iya samunshi a wannan link din https://youtu.be/nQdNN-LKZ4U, a cikin videon dayane daga cikin kwamandojin Boko Haram wanda gwamnatin Nigeria tayi musayensu da ‘yan matan Chibok mai suna #Abu_Dardaa wanda yafi shahara da #Moni ya bayyana, har ya gabatar da bayani kamar haka:

“Nine Abu Dardaa wanda akafi sani da Moni wanda arna kuka kamani a Gombe saboda na tayar muku bomabomai a cikin kasashenku na kafirci, yanzu na dawo sambisa cikin ‘yan uwana na addini, kuna Qarya kuna cewa kun Qarar da sambisa Qarya kuke, ‘yan uwana sunanan lafiya, nima ina cikin koshin lafiya, kuma ina muku gargadi da cewa kwanannan zaku ganmu akanku, ba bomb kuke tsoro ba? Bakwa tsoron Allah bakwa tsoron shirkan da kukeyi wa Allah bakwa tsoron kafircin da kukeyi wa Allah, bomb kuke tsoro? to kwanannan zakuji bama-bamai a cikin garinku
!
Abuja ne kuke bata tsaro?, kai Buhari bazaka iya da Allah ba, Buratai Qaryanka, Kuka Sheka baka isa ba, ku tuba kwai ku bautawa Allah kuyi addinin Allah kuyi abinda Allah yake so ku zauna lafiya
!
Wai kuna cewa kun sake kwamandoji kwaya biyar (5) Qaryanku, bakusan kun sake kwamandoji ba sai kunji bama-bamai a garinku, sai kunji bamabamai a church dinku, baku karar damu ba, ba wanda ya isa ya karar damu, addinin Allah mukeyi, na Allah mukeyi, wallahi bari kuji ko ran mu dubu ne daya zai fita a bayan daya wallahi sai kun ganmu a kanku”

A cikin video na biyu kuma da suka fitar wanda za’a iya gani a wannan link https://youtu.be/9OxZpyLbl2U sun nuna wasu daga cikin ‘yan matan Chibok sanye da abaya da kuma niqab kowacce tana rike da bindiga samfurin AK47, a cikin jawabin da sukeyi matan sun tabbatar da cewa sune ‘yan matan Chibok

Matan sun kuma bayyana cewa su bazasu koma gaban iyayensu ba, saboda iyayen nasu sun kafirta, sun tabbatar da cewa suma sun zama asalin rikakkun ‘yan Boko Haram

Abu na farko da zamu lura dashi shine munsan wannan wata sabuwar hanyace ta yaudara wanda ‘yan ta’addan Boko Haram suke amfani dashi domin su tsorata al’umma, barazanace ta banza sukeyi a halin yanzu, suna cika baki wai zasu tayar da bamabamai a cikin kasa, idan ma ya tabbata dagaske zasuyi hakan inaga wannan tamkar wata satar amsa ce suke baiwa jami’an tsaronmu, wanda hakan kuwa zaisa kungiyar ta Boko Haram ta rasa nasarar abinda sukayi kudurin zasu aiwatar a cikin kasa

Wannan dai shine kadan daga cikin sakamakon farko na musayen ‘yan matan chibok da gwamnatin Buhari tayi kenan, harma daya daga cikin ‘yan Boko Haram din da sukeyiwa kungiyar hidimar daura sakonnin video a youtube Abu Bakr Sulaiman yake tabbatar min da cewa gwamnatin Buhari sai da ta hada har da makudan kudade da kuma sakin kwamandojinsu kafin suka saki ‘yan matan Chibok, kuma nan gaba zasu fitar mana da sakon video akai su nuna makudan kudaden

Abu na gaba shine, da farkon al’amari bayan an sace ‘yan matan Chibok Boko Haram sun bayyana cewa sun sayar da matan a kasuwannin bayi tsakanin kasashen dake sahara, daga baya kuma sai suka fitar da wani video suka nuna cewa wai jirgin yakin Nigeria yayi sanadin hallakar wasu daga cikin ‘yan matan na Chibok a wani farmaki da yakai ta sama cikin dajin Sambisa

To tambayar da mukeyi shin Boko Haram ta warware cinikin matan Chibok din da a karon farko Shekau yace ya sayar dasu a kasuwar bayi ne?
Sannan Boko Haram ta sake busa rai ne ga ‘yan matan Chibok din da akace mana wai jirgin yakin Nigeria ya kashe?

Me yasa kuke wasa da hankalin mutane akan ‘yan matan Chibok kuke yada karairayi da tufka da warwara akan batun su?

Sannan akwai tunanin cewa nan gaba cikin ‘yan matan Chibok da za’a sako zasu zama babban barazana ga iyayensu da kuma al’ummar kasa gaba daya

Wannan sakonni guda biyu da Boko Haram ta fitar babbar iznace ga gwamnati da hukumomin tsaronmu, a kullun shi abokin gaba musamman ‘yan ta’adda duk abinda suka bayyana koda sakon Qaryace ko gaskiya ba abune da yakamata mahukunta suyi wasa dashi ba, dole a dauki lamarin da muhimmanci sannan ayi karatun ta nutsu.

Allah Ya kawo mana Mafita.

© www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.