Ladubban Kwanciyar Barci Domin Samun Gafarar Ubangiji

Ladubban Kwanciyar Barci Domin Samun Gafarar Ubangiji.

Shin kana son Allah ya gafarta maka zunubanka baki daya kafin ka kwantabarci??

Idan kana son haka to ka kiyaye abinda Manzon Allah ﷺ yace a fada dan samun hakan lokacin da ka kazo kwanta barci.

Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Wanda ya fada lokacin da yaje kwanciya barcinsa yace;

“لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير لا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم سبحان الله والحمد لله ولا إله إلا الله والله أكبر”

An gafarta masa zunubansa ko kusakuransa,ko da sunkai yawan kumfar teku).

صححه الألباني.

Yana daga cikin ladubban kwanciya barci a sunnar Annabi ﷺ

-Yin Alwala irin alwala ta sallah
-Gyara shimfida
-Karanta suratul Fatiha
-Karanta Quhuwa da faqai da nasi sau uku uku,sannan ka kofa a hannunka sai ka shafi abinda ya saukaka ajikinka,zakayi hakan sau ukku
-Karanta suratul kafirun
-Karanta Ayatul Kursiyyu
-Karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul Baqra(wato Amanar Rasul….).
-Yiwa kanka Hisabi da yin gafara da yan uwanka dan kada ka kwanta da fishi ko haushin wani.
-Yin addu’o’in kwanciya barci
-Fadar SUBHANALLAH sau 33
-Fadar WALHAMDU LILLAH sau 33
-Fadar WALLAHU AKBAR sau 34,bayan ka kwanta barci
-Kwanciya a bangaran jiki na dama
-Kashi wuta da dukkan wani haske
-Rufe mazuban ruwa ko abinda da kofofi tare da fadar BISMILLAH lokacin rufewa
-Sanya niyyar tashi sallar Assuba
-Yin sallar wutiri lokacin kwanciya.

Allah ne mafi sani

Allah ka bamu ikon koyi da Manzon Allah ﷺ a dukkan ibadarmu.

® www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.