[Lyrics] Mawaki Aminu Ala Ya Wake Daya Daga Cikin Fitattun Tsofaffi Juman Hausa Film

Sabuwar Wakar Aminu Ala

[Lyrics] Mawaki Aminu Ala Ya Wake Daya Daga Cikin Fitattun Tsofaffi Juman Hausa Film

ABUJA
10/08/2017.
8 :15pm.

AMSHI :
DOTTI MAI DABI’UN ARZIKI,
DOTTIJO ISAH BELLO JAH.

MALAMI DA KE KOYAR DA MU
MALAMIN DA KE FADAKAR DA MU,
HAZIKIN DA KE NUSAR DA MU,
JARUMIN DA KE GOGAR DA MU,
SAHIBIN DA KE ZAN CE DA MU,
SHUGABA DA KE ZAMNI DA MU,
DALIBIN DA KE KOYO DA MU,
MASANIN DA BAI RAINA MU, MU.
BABA BELLO YA NARKE DA MU,
BA SHI NUNA KYAMA SHI DA MU.

10
JAGORA :
KHALIKI MA’ARZIRCIN SARKI,
DA CIKIN KALA YA DARAJTA JAH.

A KALAR MUTANE YA YI FARI,
WANI DAN BAKI WANI YAI SHI JAH.

YAI ADON IDANUN MAI KALLO,
YA NA NUTSUWA DAGA JA JA JAH.

MUN AMINTA DUK A ALAMOMI,
BABU WACCE TAYYI KAMA DA JAH.

KO CIKIN ALAMOMIN HANYA,
GARGADIN TSAYA NA NUNA JAH.

HAKA KO ALAMAR GARGADI,
DANJAROS ANAI DA KALA TA JAH.

ALAMI NA GOSHIN SANIYA,
YANZU KAU IDANU SA YI JAH.

KO FAGEN SIYASA IN KAGA JA,
KAYYI HATTARA BA JA IN JAH.

BARAYIN ADO A GURIN MATA,
DAJIYA SUKE DA KALA TA JAH.

SUI DIGO NA JA TSAKIYAR GOSHI,
SAI SU FENTA LEBBANSU DA JAH.

20
JAGORA :
IN SUNA ADO ZUBEN KUNSHI,
DAJIYA SUKE DA BAKI DA JAH.

WANDA ZA YA BAN KYAUTAR GORO,
DA FARI KO GWARA KA BA NI JAH.

DARAJA TA JA NI KA DARSASHE,
A GABAR DA BA MAI NUNA JAH.

NA TUNA INA KARAMIN YARO,
INKIYA NA KE DA AMINU JAH.

YANZU RAYUWA TAI MIN JIMA,
RODI RODI BABU DIGO NA JAH.

JANKANO MASOYIN ALA NE,
DOTTIJO ISAH BALLO JAH.

NAI TSUMINKA ISA DAN BALLO,
TANADIN DA ZA A KIRA SHI JAH.

NA DADE INA FATAN WAKAR,
DOTTI MAI KINAYAR NAN DA JAH.

LAMARIN BUWAYAYYE ALLAH,
YARDA YAYYI BA A NUNA JAH.

SAI DA LOKACI YIWUWAR KOMAI,
SADDA SADDA NI KAM BA NI JAH.

30.
JAGORA :
GA NI GA KA ISA DOTTIJO,
KA JIYO TAFASHEN ABU JAH.

DAN HALALIYA TA KANON DABO,
JIKA NA SIDI NA GWAMMAJA.

DAGA NAN ABUJAR TARAYYA,
MASU TARIHI DAGA GARBA JAH.

SABABI NA WAKAR BALLO JAH,
ZAKU JI SHI BA WANI JA-IN-JAH.

DOTTIJO CANCANTA TA SA,
IN YI MA YABO DAGA ABU JAH.

FARI SANNADI NA ZUMUNCI NE,
SHI YA SA NA KARFAFI BELLO JAH.

SANADI NA BIYU KO KAUNA CE
TA GAMA AMINU DA BELLO JAH.

SHARADI NA UKKU KO AL’ADA,
ADABIN BAHAUSHE BABU JAH.

SANADI NA KARSHE ADDINI,
‘YAN UWA MU KE BA NUNA JAH.

YA ISAR KU GANE GABATARWA,
WACCE TAGGABATA DA JARFU JAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.