Mace Musulma Ita Ce Ta Fi Tsafta A Duniya – Bincike

Batun sha’anin tsafta yana daga cikin muhimman abubuwan da ake fatan gani a wurin ko wace ‘ya mace saboda yanayin halittar da Allah ya yi musu. Ba kamar namiji ba, a duk wata mata suna fitar da jini (wadanda suka isa haila), sannan ga batun abin da ya shafi haihuwa da raino da sauran su. A wannan makon mun yi muku nazari kan yadda wani bincike ya gano cewa mace Musulma ita ce mafi tsafta a duniya saboda tsarin da Musulunci ya kawo musu tsakanin sabon aure da idda.

Matar da mijinta ya sake ta, ya kamata ta jira a kalla wata uku, haka ma matar da mijinta ya mutu ya kamata ta jira a kalla wata hudu da kwana 10 kafin ta yi wani auren. Idan kuma ta kasance tana da ciki , to za ta jira har sai ta haifi yaron. Wannan abu yana ba wa kimiyyar zamani mamaki bayan cewa tuntuni wannan ilimin a kwai shi cikin addinin Muslinci.

Idan muka duba zamu ga cewa a cikin halittar maza da kuma mata za mu ga akwai bambanci sosai. Idan namiji ya auri mace sai ya zo ya sake ta, to wannan zai saka ta fada cikin damuwa. Wannan zai haifar mata da rashin natsuwa, kuma zai kawo mata damuwa mai tsanani. Kimiyya ta tabbatar da cewa bayan sakin aure, a hailar farko ta mace tana jinin da ya kai kashi 32 zuwa 35 daga cikin dari. Haka ma a haila ta biyu tana jinin da ya kai kashi 67 zuwa 72, cikin na uku kuma tana jinin da ya kai kashi 99.9 daga cikin dari. Bayan haila ta uku, yana wanke wa mace mahaifarta tare da samun jini mai tsafta.

Saboda haka, yin karuwanci ga mace ko kuma kwanciya da namiji fiye da daya yana kawo cututtuka a mahifa saboda haduwar maniyyi. Yana da kyau macen da aka saka ta jira, domin zai kawu masalaha. Saboda jiran zai saka sabanin da aka samu kowa zai huce. Shi ya sa Allah S.W.T ya ce, mata su jira har na tsawon wata hudu da kwana goma.

Lokacin zai sa duk wani fushi da ma’aurata suka yi, za su huce kuma za su iya gyara tsakaninsu. Wannan al’amari shi ya sa masana daga Amruka suka yi bincike a cikin kasashe Musumi na Afirka. Sun gano cewa matan Musulmi suna auren namiji daya ne, sannan binciken ya gano cewa matan da ba Musulmai ba, suna kwanciya da namiji fiye da daya, daga biyu zuwa uku.

Wannan  ya sa suka gano cewa addinin Musulinci, shi ne  kadai addinin da ke tabbatar da kare mata da kuma al’umma gaba daya. Saboda haka matan Musulmai sun fi tsafta a duniya baki daya.

Source: https://ift.tt/2OcH1jm

Leave A Reply

Your email address will not be published.