Majalisar Din Kin Duniya Tace Ta Janye Ma’aikatan Ta Daga Arewa Maso Gabar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta janye ma’aikatanta daga arewa maso gabashin Najeriya bayan ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai wa wasu jami’anta hari a jihar Borno.

Wata sanarwa da asusun tallafawa yara na Majalisar, UNICEF ya fitar ta ce an kai wa jami’an ne hari tare da jami’an wasu hukumomin bayar da agaji na majalisar a lokacin da suka nufi Maidugri daga garin Bama inda suka kai wasu kayan agajin gaggawa a yankin.

Asusun na UNICEF ya ce an jikkata mutum biyu a harin, amma sauran jami’an suna cikin koshin lafiya.

Sanarwar ta ce Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da duk wasu ayyukan jinkai a yankin, har sai ta sake yin nazari kan yanayi tsaro.

Ita ma a wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojan Nigeria ta tabbatar da harin, har ma ta ce an jikkata dakarun ta guda biyu.

Sanarwar — wacce mai magana da yawun rundunar ta sojan Najeriya Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar — ta ce wasu ‘yan kungiyar Boko Haram ne da suka labe a kauyen Meleri kusa da garin Kawuri suka ka yi wa tawagar ma’aikatan majalisar dinkin duniyar kwanton-bauna.

Ita dai tawagar tana tafiya ne tare da rakiyar sojojin Nigeria, wadanda Kanar Sani Usman ya ce sun mayar da martani kan ‘yan Boko Haram din, har ma suka fatattaki maharan na Boko Haram har zuwa shiyyar Afunori.

Sanarwa ta soja ta ce tana jajanta wa jami’an na Majalisar Dinkin Duniya da ma jami’anta da suka jikkata a farmakin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.