Majalisar dokokin jihar Kano ta tsige shugabanta

Majalisar dokokin jihar Kano ta tsige kakakinta, Yusuf Abdullahi Ata inda ta maye gurbinsa da tsohon kakakin majalisar Kabiru Alahsan Rurum.

Rurum ya yi murabus daga shugabancin majalisar a watan Yulin shekarar 2017 bayan da aka tuhume shi da aikata rashawa.

Labaran Madari, mamba mai wakiltar karamar hukumar Warawa shine ya gabatar da kudirin tsige Ata inda ya samu goyon bayan Abdullahi Muhammad dan majalisa daya tilo na jam’iyar PDP dake majalisar.

A yau ne majalisar dokokin mai wakilai 40 ta dawo daga hutun wata biyu da ta yi.

A ranar 14 ga watan Mayu yan majalisar 24 suka fara yunkurin tsige kakakin majalisar kafin daga bisani gwamnan jihar ya shiga tsakani.

Source: https://ift.tt/2KcJVlA

Leave A Reply

Your email address will not be published.