Makafi masu digiri suna zanga zanga a kofar gidan gomnatin jihar IMO

Zugar matasa makafi wadanda suka kammala karatun jami’a sun kewaye kofar gidan gomnatin jihar IMO suna kiran Gomnan jihar Rochas Okrocha akan rashin kulawa dasu da kuma samar musu aikin yi. 
Makafin sun kewaye gidan gomnatin ne suna korafin cewa gomnati bata lura dasu kuma ana musu wariya wajen daukar aiki a jihar. 
Daya daga cikin makafin ya bayyana cewa akwai makafi dayawa a jihar wadanda sun kammala karatun digiri amma basuda aikinyi saboda gomnatin tana nuna halin ko in kula akan su. 
Yace “Dukda nakasarmu muka daure mukayi karatu kamar yadda masu ido sukayi to mezaisa bazaa samar mana aiki ba?  Ko kuma mu ba ‘yan adam bane?  Shin anason muje muyi bara ne? A gaskia ina kira gomnafi ta duba wannan lamari. 
Haryanzu dai gomnatin jihar bata maida martani ba kan bukatarda matasan suke nema da kuma abinda suka kira rashin adalci tsakaninsu da masu ido. 

Source: https://ift.tt/2MN2m2j

Leave A Reply

Your email address will not be published.