Matar Direban Adaidaita Sahu Ta Haifi ‘Yan Biyar A Anambra

Wata mata ‘yar shekara 25, Mrs Ndidi Odo, ta haifi ‘ya’ya biyar a garin Nnewi, Jihar Anambra.

Mai jegon ta haifi jarirai biyar ɗin a asibitin ‘God’s Mercy Hospital’ da ƙke Obiuno, Otolo-Nnewi.

Daruruwan mutane ne suka yi dandazo a asibitin domin ganin mai jegon da ‘yan biyar ɗin nata.

Uwar jarirai biyar ɗin (huɗu maza da mace ɗaya) ta ce bata san tana ɗauke da ‘ya’ya biyar a cikinta ba. Abin da dai ta sani shi ne hoton cikin nata da aka yi ya nuna tana ɗauke da ‘yan biyu.

Take cewa, a baya ta haifi ‘ya’ya mata guda uku waɗanda ta haifa daban-daban. Kafin su kuma ta haifi ‘yan uku a tare; maza uku da mace ɗaya.

Sai dai take cewa daga baya dukkan mazan sun mutu inda mata guda huɗun sukai saura. A cikin nata na karshe ne take ta fatan ta haifi ɗa namiji domin ta tsira da ‘ya’ya mata huɗu da namiji ɗaya.

Mrs Odo, mai koyon aikin tela, wacce ta haifi ‘yan biyar ɗin ta hanyar tiyata, ta ce tana cikin koshin lafiya amma tana bukatar taimako daga al’umma saboda iyalin nata ba zasu iya ɗaukar nauyin ‘ya’ya tara ba.

Wata malamar asibitin da akai haihuwar, Blessing Odemena, ta bada labarin yadda mai jegon ta zo gurinta tana cewa ba abin da take matukar muradi sama da ta sami haihuwar ɗa namiji.

Take cewa, abin mamaki, da aka ɗau hoton cikin sai aka gano ‘ya’ya biyu. Da cikin ya kara girma sosai sai likita ya ce a kara ɗaukar hoton cikin. Da aka ɗauka sai kuma aka gano uku.

Mahaifin ‘ya’yan, Mista Abuchi Odo, wani direban babur ɗin Adaidaita Sahu, ya ce a baya ya so ya tsere sakamakon ganin babban nauyin da ya hau kanshi, amma daga baya yayansa da wani mutum mai suna Prince Justin Brown suka taushe shi a kan kar ya gudu.

Ya ce tsohon babur ɗin shi ba zai iya ciyar da shi, matarshi da ‘ya’ya tara ba.

Sai dai ya mika kokon bararshi ga gwamna Willie Obiano, Mista Peter Obi, Cletus Ibeto, Dakta Ifeanyi Uba, Sir Louis Onwugbuenu, Dame Virgy Etiaba, Archbishop Godwin Okpala, Bishop Hilary Okeke da sauran masu hannu da shuni na jihar da ma wajen jihar kan su taimaka masa.

Source: https://ift.tt/2LGUAKj

Leave A Reply

Your email address will not be published.