Mu Shakata Tare Da Mairo Muhammad Mudi Da Ashiru Abdulqadeer

Mu Shakata Tare Da Mairo Muhammad Mudi Da Ashiru Abdulqadeer

MAI DOYA        
    
Wata rana ce, wani alkali yana warware wata shari’a kansa ya yi zafi sai wani bakauye mai tallar doya ya zo wucewa ya leko cikin kotun ya ce, “A sai doya!”

Alkali ya ce a zo masa da mai doya. Ya ce masa,  “ka san ko surutu ba a yi a kotu amma ka zo kana tallar doya? saboda haka za a daure ka a gidan yari tsawon wata uku.”

Mai doya yace, “daga cewa a sai doya?”

Sai alkali ya ce, “wata shida.”

Mai doya ya sake cewa, “doya fa na ce a saya.”

Sai alkali ya ce, “wata tara.”

Ran mai doya ya baci ya ce, “to a sai doyoyi.”    

ABIN SHA’AWA ABIN KOYI
Akwai wata tsohuwa,  tana da ‘ya’ya goma duk maza ne amma kuma suna ji da ita, kowa a ‘ya’yan suna iya kokarinsu su faranta mata rai.

A cikin ‘ya’yan duk ta fi son dan’autanta wanda shima magidanci ne. Watarana ana bikin a gida aka fito mata da kujera ta zauna a bakin kofarta ana ta aikin biki,  jikoki na ta tsokanarta amma ba ta ce masu uffan ba.

Sai aka ji ta fashe da kuka,  surukai na ta tambayarta, jikoki kuwa sai raha suke . Can sai ta ce ta ga kowa yana kai yana dawowa amma ita ba ta ga dan autanta ba. Aka yi ta ba ta hakuri aka ce yana nan tafe amma sai share hawaye ta ke.

Can sai aka ji an bude masa get ya shigo da motarsa,  jikokinta suka tarbe shi tun bai fito daga mota ba suna cewa,  “Baffa,  mamanka na nan tana ta kuka wai har yanzun ba ka iso ba.”

Ya bude mota ya wuce su da sauri ya je ya same ta,  tana share hawaye, “Inna yaya kike kuka? “

“Na ce ban ganka ba tuntuni.”

“To share hawayenki kawai, na taho.”

Daganan sai aka ga ya dauko ta a hannuwansa kamar yadda uwa za ta dauki jaririnta ya shige dakinta da ita sai ga shi ya fito da ita a bayansa ya goya ta da zani, ita kuwa ta makale kanta a bayansa tana murmushi.  Jikoki suna ta ihu sai ya ce,  “na rasa me zan mata ta ji dadi,  ba ta iya cin nama ko wani abu mai dadi,  na rasa irin kayan da zan saya mata ta ji dadinsu sai na lura goyata kawai zai ba ni kwanciyar hankali,  sannan kila na dace ta ji dadin haka.”

©Zuma Time Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.