Musha Dariya Labarin Malam Shehu Jaha Da Barawo

Wata Ranane  Malam Shehu Jaha Yayi Dogon Zango Da Dare Baiyi Barciba Yana Zaune  Sai Yaji Buruntu Cikin Daki, Sai Ya Fahimci Cewa Lallaifa Barawo Ne Ya Shigo Cikin Dakin Nan.

Nan Take Sai Shehu Ya Samu Wuri Ya Boye,  Shiko Barawo Sai Ci Gaba Buruntu Da Bincike Bincike Yakeyi Bai Samu Komaiba.

Sai Ya Daga Kai Daga Sama Saiya Hangi Wata Yar Durowa Jingine A Jikin Bango, Sai Barawo Yayi Wuf Ya Nufi Inda Durowar Nan Take Da Nufin Koya Samu Wani Abu A Ciki.

Sai Yasa Hannu Ya Fincike Kofar Durowar Da Karfi Budewarsa Keda Wuya Kawai Sai Yayi Arba Da Malam Shehu Jaha A Ciki , Nan Take Sai Yayi Karfin Hali Irin Nasu Na Barayi Yace Malam Kaiko Me Kakeyi Cikin Daren Nan Anan.

Da Budar Bakin Malam Kuwa Sai Yace , Ranka Ya Nayi Hakan Ne Kawai Sabo Da Karda Ka Zargeni Koka Rikeni A Zuciyarka, Sabo Da Nasan Bazaka Samu Abunda Zaka Sata A Cikin Gidan Nanba , Saboda Hakane Yasa Na Buya Sabo Da Jin Kunyar Ka .

Hahaha Hahaha hahaha hahaha haha .

Leave A Reply

Your email address will not be published.