Nafisa Abdullahi Akwai Sirri Tsakanina Da Adam A. Zango

Jarumar Wasan Hausa Film Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Dalilanta Na Kin Fitowa A Wani Sabon Film Mai Suna RARIYA Wanda Jaruma Rahama Sadau Ta Shirya.

Jarumar Ta Bayyana Hakan Ne Cikin Wata Fira Da Sukayi Da Shafin “Kannywood Scene” Inda Jarumar Tace Taki Karbar Aikin Film Dinne Saboda Aikin Wani Sabon Film Da Takeyi Mai Suna Labarina Wanda Aminu Saira Ya Shirya.

Sannan Dangane Da Tsakanin Ta Da Adam A. Zango Jarumar Tace Bazata Iya Fadin Duk Abubuwan Tsakanin Ta Da Jarumi Adam A. Zango Ba Saboda Ba Komai Ne Zata Rinka Fitowa Kafafen Yada Labarai Tana Fadiba, Domin Kuwa Komai Na Rayuwa Yana Bukatan Sirri Ballantana Tsakanin Ta Da Adam A. Zango.

Sannan Ta Kara Da Cewa Itafa Yanzu Ta Kama Gabanta, Kamar Yadda Shima Adam A. Zango Ya Kama Gabanshi Kan Batun Soyayyar Su Ta Baya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.