Obasanjo ya sake komawa jam’iyyar PDP

Tsohon shugaban Nigeria Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP wacce ya fice daga cikinta a shekarun baya. 
Obasanjo ya bayyanawa manema labarai cewa ya fita daga jam’iyyar ne a abaya saboda rigingimu da suka addabi jam’iyyar wanda yake ganin ‘ya’yan jam’iyyar sunyi masa laifi saidai ayanzu kuma an daidaita ya yafe duk abinda akai masa a baya. 
Obasanjo ya dawo jam’iyyar ne tareda dayawan membobinsu na jamiyyar ADC wacce ya kafa a kwanakin baya. 

Obasanjo ya bar jam’iyyar PDP ne a shekarar 2014 ya yaga katinsa na  zama a jamiyyar. Lokacinda ya bar jam’iyyar ya ayyana zai zauna matsayin uban kasa kawai ya daina shiga sabgar siyasa, Ya kuma bada goyon bayansa ga shugaba muhammadu Buhari.

A baya bayannan kuma ne suka  samu sabani da Shugaba Buhari abinda ya ingiza Obasanjo komawa cikin harkokin siyasar kasar.

Source: https://ift.tt/2KAO6I6

Leave A Reply

Your email address will not be published.