Rahama Sadau : Tun Ina Karama Nake Burin In Zama Yar Rawa DANCER

 Rahama Sadau

Tsohuwar Jarumar kamfanin shirya fina-finan Hausa wato (Kannywood) Rahma Sadau tace tun tana Yarinya yar Karama bata da wani Burin daya wuce ta zama me yin Rawa.

Jaruma Rahma Sadau ta bayyana haka a wata hira da tayi da daya daga cikin Gidajen Talabijin na Arewacin kasar nan.

Tace tana kasancewa cikin nishadi duk lokacin data samu kanta tana yin Rawa, gashi kuma yanzu ta wuce matsayin Rawa ma.

Idan baku manta ba yanzu haka hukumar ladabtarwa na kamfanin shirya Fina-finan Hausa wato Moppan ta dakatar da Jarumar daga fitowa cikin shirye-shirye fina-finan Hausa tun bayan wani faifaiyin bidiyo daya fito wanda Jarumar tayi waka da wani mawaki me suna Classic.

Wanda A Halin Yanzu Haka An Riga Da Anjanye Wannan Kora, Kuma Kwanan Nan Jarumar Zataci Gaba Da Fitowa A Sababbin Fina-finai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.