Sanatoci Bakwai Sun Kammala Shirin Komawa Jam’iyyar APC Daga PDP

Sanata Mohammed Ali Ndume dake wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu a jam’iyyar APC ya ce kawo yanzu akalla ‘yan majalisu bakwai ne daga PDP suka kammala shirin su na komawa APC.

Ndume, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ke hira da ‘yan jarida ya ce iya kwarewa a fagen siyasa ne ya sanya har yanzu jam’iyyar ta APC ke da rinjaye.

Sanata Ndume ya kara da cewa sauyin shekar da aka samu a zauren majalisar a makon da ya gabata ya koya masu hankali inda yanzu suka kara zama tsintsiya madaurin ki daya.

Source: https://ift.tt/2AlBLIc

Leave A Reply

Your email address will not be published.