Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi Ya Soki Buhari Kan Tattalin Arziki

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya yi suka ga yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke tafiyar da tattalin arzikin Najeriya.

Sarkin, wanda ke jawabi a wurin wani taron tattalin arziki a ranar Laraba a birnin Kano, ya ce idan shugaban bai yi hattara ba to gwamnatinsa za ta kasance ba ta da maraba da wadda ta shude ta Goodluck Jonathan.

“Idan wannan gwamnatin ta ci gaba da yin abubuwa kamar gwamnatin da ta shude, to za mu kare irin yadda ta kare,” kamar yadda shafin Premium Times ya rawaito.

“Ita gaskiya daci gare ta. Amma kuma dole ne ku saurare mu,”a cewar Sarkin.

Ya kuma shawarci gwamnati da ta mayar da hankali kan neman wasu hanyoyin samun kudin shiga tare da karfafa gwiwa wajen zuba jari.

Tattalin arzikin Najeriya na fuskatar koma-baya saboda faduwar farashin man fetur da kuma darajar kudin kasar.

Shi dai Shugaba Buhari ya sha bayyana aniyar gwamnatinsa na sauya fasalin tattalin arzikin kasar da kuma rage dogaro kan albarkatun man fetur.

Tsohon shugaban babban bankin kasar ya kuma gargadi gwamnati da ta daina ba ta lokacinta wajen dora laifin lalacewar al’amura kan gwamnatin da ta shude, abin da ya kamata ta yi a cewarsa, shi ne ta fuskanci kalubalen da ke gabanta.

“Ba lallai sai masanin tattalin arziki ne zai san cewa dukkan tsarin da ya amince mutum ya samu makudan kudade kawai saboda ya buga waya, ba tare da ya zuba jarin ko taro ba, tsari ne mara kyau, kuma ba zai dore ba,” in ji Sanusi.

Ya kuma kara da cewa dole gwamnatin Buhari ta duba manufofinta na tattalin arziki, ta kuma amince da cewa akwai wadanda ba sa aiki, sannan ta daura damarar gyara su, idan ba haka ba a koma ruwa.

Sarkin na Kano ya kuma soki irin mutanen da ke bai wa shugaban kasar shawara kan harkar tattalin arziki da cewa ba na kwarai ba ne.

Mutane da dama a kasar na kallon Sarki Sanusi II, a matsayin mutum mai yawan janyo cece-kuce, kuma mai tsage gaskiya komai dacinta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.