Sarkin Kano Ya Dauki Nauyin Mahaddacin Alku’anin Nan Da Za’a yiwa Dashen Koda.

Sarkin Kano Ya Dauki Nauyin Mahaddacin Alku

Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, ya dauki nauyin mahaddacin Alkur’anin nan da aka ce zai a yi wa dashen koda.

A cewar Sa’adatu Baba Ahmad, a kwanaki biyu da suka shude ne ta ga Real Fauziyya D. Sulaiman ta buga labarin neman taimako tare da halin ha’ula’in  da wannan bawan Allah ke ciki, a shafinta inda ita Hajiya Sa’adatu ta mika wannan sako wajen mai martaba.

Da mai martaba ya gani sai ya umurce ta da ta je ta duba shi inda ya dauki alkawarin zai biya Naira miliyan 6 da Aminu Kano suka bukata domin ceto mahaddacin Alkur’anin.

“Tun safiyar wannan rana Mai Martaba ya tura asibitin Aminu Kano da Nassarawa in da marar lafiyar Na’if Ismail, ya ke aka shirya komi don ci  gaba  da kula da lafiyarsa.

“Da yammacin yau kuma ya yi tattaki da kansa zuwa duba marar lafiya ya yi masa addu’ar samun lafiya tare da fatan Allah Ya tashi kafadunsa.”

Hajiya Sa’adatu ta ci gaba da cewa, abinda ya fi ban tausayi shine marar lafiyar nan ya dauki Alkur’aninsa ya  danka wa Mai Martaba Sarki inda ya ce, “wannan ne abinda na ke da shi kuma na baka.”

©Zuma Times Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.