Sarkin Musulmai : Cristoci Sunfi ‘Yan Ta’adda Ai Kata Miyagun Laifuka

Sarkin Musulmi
Sultan na jihar Sokoton Alhaji sa’ad Abubakar na III ya bayyana cewa duk da cewan ba’a yarda cewan Kiristoci yan ta’adda bane amma suna aikata mukayen laifuka ga dan Adam.

Sa’ad Abubakar na III yayi Magana a babban birnin Benin a taron majalisa na kungiyar Nigeria Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA).

Abubakar ya yaba ma kungiyar da sukayi sanarwa mai karfi dake kare addinin Islama a matsayin addinin zaman lafiya. A kan maganar sanya hijabi, ya bayyana cewa sanya hijabi hakki amma ba dama ba ga musulmai a fadin kasar.

Sultan yace: “Hijabi hakkin mu ne ba wai dam aba. Ba alfarma bane a gare mu. Hakkin mu ne. “Kuma muna amfani ne da kundin tsarin mulkin Jumhuriyyar Najeriya da ya bayar da daman yin bauta.

“Shi yasa bamu takura wa kowa dake son yin bauta yanda yake so ba.”

Ya kara da cewa: “Kasar Najeriya kasa ce da ake addinai da dama, ba wai addini day aba. Kuma a matsayin ta na kasa mai addinai da yawa, dolene mu bari ko wani addini ta ci gaba a yanda take ba wai mu take hakkin juna ba, wanda yake nufin cewa dole a bari nayi addini na kamar yanda da na yarda da umarnin da Al-Qur’ani mai girma ba wai wani abu ba.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.