Sauya Sheka: Komawar Gwamna Ortom Zuwa PDP Ya Ba Mu Mamaki Sosai – APC

Jam’iyyar APC ta ce, ta yi mamakin sauya shekar da Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya yi zuwa jam’iyyar PDP.

A cikin wata sanarwa da kakakin APC Bolaji Abdullahi ya fitar, jam’iyyar APC ta ce gwamnan ya fice ne yayin da shugaban ta Adams Oshiomhole ke kan kokarin magance matsalolin da gwamnan ya gabatar game da siyasar jihar Benue.

Jam’iyyar APC, ta ce ta yi mamakin ficewar gwamnan, bayan ya nuna cewa ya gamsu da tabbacin da shugaban jam’iyyar ya ba shi a ganawar da su ka yi dangane da shawo kan matsalolin.

Gwamna Ortom dai ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC ne, yayin da ake gudanar da wani taron shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a birnin Makurdi, bayan wasu matasa sun hana shi zuwa Abuja don halartar wani taron sulhu na jam’iyyar APC.

Source: Alummata.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.