Shahararrun ‘Yan Wasan Hausa Film Guda 5 Da Irin Baiwar Da Allah Yayi Musu

Mutane da yawa suna ma ‘yan wasan fina-finan Hausa kallo a iyaka fitowa a fim. Mun danyi muku bincike sannan mun kawo muku jerin wadansu 5 daga cikinsu wadanda suke da wadansu basiran banda fitowa a fina-finai.

1= BELLO MOHAMMED BELLO

wanda bayan shiryawa ya iya yaruka kusan 19 a yarukan duniya, Mawaki ne, Marubucine, Darektane, mai shiryawane da dai sauransu.

2= ALI NUHU

Ali Nuhu yana daga cikin wanda ya fi kowani dan wasan fina-finan Hausa karbar Kyaututtuka a harkar finafinan. Bayan haka kuma yana iya magana da yaruka kamar Indiyanci, larabci, yaren faransanci daidai iya gwargwado.

Bayan fitowa da yakeyi a fina-finai, Ali yana shiryawa, Darekta ne sannan wata baiwa kuma da yake dashi itace na karantar da kananan aktoci yadda ake shirya fina-finai.

ADAM ZANGO

Gwanin rawa, kuma mai shiryawane, sannan Darektane, mawaki, sannan edita ne. duk wadanna baiwace wanda Adam zango yake dasu bayan fitowa da yakeyi a fina-finan Hausa.

Adamu mai saukin kaine sannan mai taimakon Jama’ane wanda binciken mu ya nuna ya na da hakuri da tausayi.

4= SANI DANJA

Sani Danja mashahurin Mawakine sannan dan Kasuwa ne na gaske. wannan baiwace da yake da ita wajen sarafa fasaharsa zuwa ga Kasuwanci da iya mua’mulla da mutane da dai sauransu.

6= RAHAMA SADAU

Kallabi tsakanin rawuna, Rahama ta kware wajen rawa tun kafin ta shigo harkar fina-finai wanda mutane da yawa basu sani ba. Rahama marubuciyace sannan gwanar ado ce inda take da kamfanoni na kwalliya a arewacin Najeria.

Ta na harkar fina-finan Nollywood.

Leave A Reply

Your email address will not be published.