Shin Da Gaske Ne Jaruma Jamila Umar Ta Mutu ?

Jamila Umar 

Wai shin da gaske ne jaruma jamila umar nagudu ta mutu.

Hakika dukkan me rai mamaci ne, kuma hakika dukkan rai sai ta dandani zafin mutuwa.

A dai ranar juma’ar data gabata ne aka wayi gari da yada wata jita jita mai kama da jurwaye wurin wanka.

Inda jita jitar take ta yawo a kafafan sada jumuntar yanar gizo gizo dama wasu manyan garuruwa da biranan wannan kasa tamu ta Nigeria harma da makofta.

Inda ake ta cewa Allah yayiwa jarumar Jamila Umar Nagudu rasuwa. Hakan kuwa ya samo asaline,  biyo bayan wani faifan video da jarumar ta wallafa a shafinta  na Instagram.

Inda Videon yake nuni da cewa jarumar tana neman Addu’ar daukacin masoyan ta game da tafiyar da zasuyi tare da yan uwanta daga garinsu na kano zuwa Kaduna.

Gadai martanin da jarumar ta mayar game da wannan jita jitar da ake yadawa.  Danna  wannan hoton dake kasa domin kallon cikakken bayanin da jarumar tayi a shafin Youtube.

Inda a karshen jarumar ta bayyana cewa tana nan a raye kuma tayi kira da jama’a cewa don Allah a guji yada jita jita, sannan kuma a rinka bin diddigin labari musamman iri iren wadan nan kafon a yarda dasu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.