Shin Fafutukar Kafa Kasar Biafra Sukeyi Ko Kisan ‘Yan Arewa ?

Biafrans Killed Upto 40 Northern Hausa Fulani Today

Shin Fafutukar Kafa Kasar Biafra Sukeyi Ko Kisan ‘Yan Arewa ?

BIAFRA KO RAINA GWAMNATI ??

Daga : Yarima Gangariya

A yau Ne Wasu Gungun Matasan Jihar Enugu Masu Ja Da Gwamnati Suka Fito Kamar Yanda Suka Saba Abaya Don Yunkurin su na ballewa daga Tarayyar nigeria don kafa wata Kasar su wacce suka lankayawa suna BIAFRA ko Nace ake kiran su da yan BIAFRA inda suka farwa mutane musamman yan arewacin nigeria ko baro baro nace Hausawa inda suka samu nasarar cika Mummunan nufinsu na salwantar da rayukan da a dazun misalin karfe 2 biyu Agogon 🇳🇬 nigeria wani ganau jiyau yace sun kai rayuka arba’in da uku wanda mafi yawan su Hausawa ne musulmai yan arewa

Wanda hatta wannan rubutun danayi nayi shine adaidai gaɓar da muka samu guri muka fake da akan hanya ta ta komawa gurin aiki CROSS River State Calabar on tsira daga wannan ta’addancin wanda Da’ace daga arewacin nigeria wannan abun ya faru da babu wani uzuri ko suna da za’a lankayawa wayanda suka aikata wannan ta’asa sai YAN TA’ADDA
Tunda Daman can duk wani musulmi agurin su dan ta’adda ne

Bama goyon bayan zalunci da ta’addanci muna Allah wadai dashi daga duk inda ya fito
Saidai muna mika kokon barar mu zuwa ga hukumar dake da alhaki akai dasu gaggauta daukar Tsatstsauran matakin dakile wancan ta’addanci tareda kawo karshen faruwar wannan don Allah ku taimakawa bayin Allah dake ire iren wayancan gurare

Anan arewa babu wani matashi dake hana wata qabila neman abincinsa duk kuwa da kaka gidan da sukayi a kasuwancin mu arewa ciki harda sana’ar gado ta iyaye da kakanni zaka samu kabilun kudancin kasa sun shige ta sunyi Kane Kane.

Leave A Reply

Your email address will not be published.