Shin ko kasan abunda launin fitsarin ka ke nuni game da lafiyar ka

Shin ko kasan abunda launin fitsarin ka ke nuni game da lafiyar ka

Shin ko kasan abunda launin fitsarin ka ke nuni game da lafiyar ka

B.Abubakar

shi dai fitsari kusan kashi 95 ruwane wadanda qoda ke tacewa dake dauke da abubuwa kamar su Urea,choloride sodium,potassium,uric acid da sauransu.A mafi yawa yana da launin dorawa(yellow coloration)

fitsari wata hikima ce ta Allah inda abubuwa marasa amfani masu cutarwa ke fita daga jikin dan adam.Wanda rashin yin fitsarin musibace dake matukar barazana ga lafiya da rayuwar dan adam kanta.

Da yake bakowa keda hikimar kula da canzawar launin fitsarinsa ba wanda lokuta da dama hakan na nuni ga wasu rashin lafiyoyi ko wasu sauye sauye da jiki ke samu a halin rayuwar yau da kullum.
Abubuwa ukku ne suke da alhakin sauya launin fitsarin mutum kamar 1 -Shan maganin bature wanda ake kira Antibiotic kamarsu : Nitrofurantion,warafin,rifampin,da sauransu.
2- Abincin da muke ci da qaramcin shan ruwa.

3- Rashin lafiyoyi.

To a duk sanda kassan baka shan wani maganin bature mai sauya launin fitsari to akoi bukatar ka lura da kyau akan launin fitsarinka saboda zai iya nuni da cewa akoi wani abu dake damunka a badini.

Kamar dai yanda kuke gani akan hoton dake zuwa akoi bayani daki daki kan kowane launin fitsari.Harwayau kuma a kula bai zamo doleba dan kaga kana fama da daya daga cikin matsalolin nan shi ne ke tabbatar maka da cewa lallai baka da lafiya ba,dan kada kaje kayi ta faman wasu qwayoyi da sunan kana fama da wata rashin lafiyar da baka da tabbas akanta ba.Abu mafi kyau anan sai aje aga likita ayi bincike idan da matsala akoi shawara da maganin da ya dace a bayar.

1.Transparent :Fitsari fari kal marar launi kenan,yana nuni da qaramcin ruwa a jiki (dehydration) dan haka idan an lura da wannan matsalar sai a yawanta shan ruwa akai akai,amma fa a tabbatar an yiwa ruwan tubali ma’ana aci abincin da zai sa aji ana bukatar yawan shan ruwa.kada a afkawa ruwa ayi ta zuqa wahala ake yi dan basa zama a ciki.

2.Pale yellow : wannan launin dorawa marar duhu yana nuna ba matsala(Normal)

3.Drark yellow : Normal ne amma da bukatar a yawaita shan ruwa dan kare afkuwar dehydration.

5.Brownish orange : Inba da matsala dehydration ba to akoi alamun ciwon hanta (liver disease)

6.Pinkish red : fitsari mai launin ja yana nuna alamun ciwon koda (kidney disease) da ciwon da ake ki Urinary tract infection ko wani rauni  (tumor)

7.Blue / green : wata cuta ce daba safai ake samunta ba asali akan gado tane.

8.Foamy : Alamun cutar koda kenan.Sai aje ayi bincike dan kara tabbatarwa.

Alhamdulillah

Leave A Reply

Your email address will not be published.