Shugaban Hukumar Tace Fina Finan Hausa Ya Zama Jakadan Zaman Lafiya

Ismail Afakallahu
Isma’il Na’abba Afakallahu Shugaban Hukumar Tace Finanan Hausa Ya Zama Jakadan Zaman Lafiya.

Daga Sharfuddeen Baba, Kano.

Ranar Juma’ar data gabata aka yi bikin karrama wasu mashahuran mutane da lambar karramawa ta Jakadan Zaman Lafiya, an gudanar da taron a garin Jos shelkwatar Jihar Filato. Shugaban Hukumar Tace finafinai ta Jihar Kano Malam Isma’ila Na’abba Afakallah shima yana cikin wadanda suka yi hafzi da wannan gagarumar lambar yabon.

Ko shakka babu kasancewar Isma’ila Na’abba Afakallah na cikin jagororin masana’antar shirya fina-finai Hausa data Jihar Kano, idan akayi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar abaya tun lokacin yana rike da shugabancin Kungiyar Arewa Fim Makers, har kuma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ga irin gudunmawar da masu shirya fina-finai suke baiwa gwamnatinsa, hakan tasa gwamnan zabarsa tare da damkasa jagorancin hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a hannunsa.

Wata Kungiya mai suna Peace Federation ne suka zakulo wadannan mashahuran mutane kuma suka amince da basu wannan lambar karramawa mai tarin muhimmancin a irin wannan lokaci. Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban hukumar tace fina-finan ta Jihar Kano Malam Isma’ila Na’abba Afakalla, tsohon shugaban Kungiyar Arewa Film Makers Association, kwararren malamin Islamiyya, Jarumi, producer da dai sauran mukamai da Allah ya amince masa dasu, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda wannan Kungiya ta zabosu tare da basu wannan lambar karramawa ta Jakadan zaman lafiiya.

Afakallah yace ni ban sansu ba, ashe su suna biye da irin rawar da muke takawa, wannan kuma shi ne hakikanin gaskiya, don daman kamata ya yi wadanda ake al’amari dominsu sune a hakku su shaidi mai yin irin wannan hidima.

Saboda haka sai ya mika godiyarsa ga wannan kungiya tare da tabbatar masu da cewar zai kara kaimi wajen hidimtawa al’umma gwargwadon iko, haka kuma ya godewa mai girma Gwamna Ganduje musamman ganin yadda yake kulawa da abubuwan da ko shakka babu suke amfanar al’ummar Kano da Kanawa, yace hukumar sa tana nan kan bakarta na tabbatar da ingancin duk wani fim da ake son ya shiga al’umma, sannan kuma suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin an tsarkake sana’ar shirya fina-finai. A karshe ya godewa masu shirya fina-finai saboda irin goyon bayan da suke baiwa wannan hukuma.

Leave A Reply

Your email address will not be published.