Shugaban Kasa Buhari Ya Rantsar Da Masu Bashi Shawara

buhari

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari, ya rantsar da wasu sabbin masu ba shi shawara na musamman a ranar Laraba.

Wadanda aka rantsar sun hada da Dokta Adeyemi Dipeolu a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman a kan al’amuran tattalin arziki, da Alhaji Tijjani Abdullahi, wanda aka bai wa muƙamin mai ba da shawara na musamman a kan tsare-tsare.

Barrista Maryam Uwais kuma ita ce mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman a kan raya al’umma.

Yayin da Sanata Babafemi Ojodu ya zama mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman a bangaren sha’anin siyasa.

An dai daɗe ana ƙorafi a kan cewa Shugaba Buhari ba shi da masu ba shi shawara a kan wasu muhimman al’amura, abin da ake ganin yana jawo tsaiko wajen tafiyar da ayyukan da shugaban ƙasar ke gudanarwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.