Sojoji Naci Gaba Da Farautar Tsagerun Niger Delta A Jihar Legas

Dakarun hadin gwiwa na sojin sama da na kasa da kuma ruwan Naijeriya na ci gaba da kai farmaki akan matasan nan da ake zargi na addabar garuruwan da ke jihohin Legas da kuma Ogun.

Daukar wannan mataki ya zo a sakamakon yadda ake zargin matasan da suka fito daga yankin Naija-Delta da kai hare hare a yankunan da kuma satar man fetur daga bututun man fetur da suke fasawa.

Rahotannin na cewa Fiye da matasa dari daya ne da ke satar man fetur suka rayukansu a yayin wannan samame, sai dai kuma jami’an tsaro sun musanta kashe wani.

Mazauna wadannan yankuna wadanda ga dukkan alamu ke cikin zaman dar-dar, sun nuna jin dadinsu bayan dawo da zaman lafiya da dakarun tsaron suka samar a yankunan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.