Sojoji sunyi nasarar maida ‘yan gudun hijira 5,000 gidajensu a zamfara

Rundunar sojan Nigeria sun bayyana jindadi gameda nasarar da suka samu na kakkabe ‘yan ta’adda da suka addabi jihar zamfara.

Rundunar tace yanzu haka kimanin mutane  5,000 y’an gudun hijira sun koma cikin gidajensu.

Rundunar soja mai suna “Operation Sharan Daji” ta gudanarda wani samame a wani daji da maharan ke boyewa aciki. Samemen yayi sanadiyyar hallaka mahara dadama.

Kwamandan Rundunar sojan Muhammad Muhammad ya zanta da manema labarai inda yace “Yanzu haka dayawan ‘yan gudun hijira sun koma gidajensu musamman mazauna yankunan Galadi, Kwaddi, Kauyen Katuru suke cikin kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.

Rundunar sojan ta kuma gabatarda sabon kwamanda mai suna OLABANJI shine zai cigaba da rike sojojin “Operation Sharan Daji” wadanda zasuyi aiki jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto domin dakile ta’addanci a duk sassan yankunan.

Rundunar sojan ta kuma ce yanzu haka suna cigaba da neman maharan da suka arce cikin dazunan zamfara kuma sojoji na cigaba da binciko su aduk inda suke boye.

Source: https://ift.tt/2OoHSO5

Leave A Reply

Your email address will not be published.