Sojojin Saman Nigeria Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Ba A dadi.

Sojojin Saman Nigeria Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Ba A dadi.

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce wani jirgin yakinta da ke cikin shirin Zaman Lafiya Dole ya kai hare-hare kan wata maboyar wasu ‘yan Boko Haram, inda ya kashe da dama a cikinsu.

Wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Air Commodore Olatokunbo Adesanya ya fitar, ta ce jirgin yakin ya yi luguden wuta a kan maboyar, wadda ke yankin Parisu a dajin Sambisa, a ranar Talata.

A cewarta, harin ya biyo bayan wani gungun ‘yan Boko Haram da aka hango suna taruwa a karkashin wata bishiya kusa da wani gini, inda aka yi amfani da rassan bishiya wajen rufe maboyar.

Ta ce jirgin yakin ya fara yin luguden wuta a kan maboyar wadda bayanai suka nuna cewa mayakan Boko Haram ne, kafin kuma ya kai hari a kan wani gini shi ma da yake kusa.

Source: BBC hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.