Ta’addanci : Kamfanin Twitter Ya Rufe Shafukan Mutane Dubu 235, 000

Kamfanin Twitter na sada zumunta a yanzar gizo ya sanar da rufe shafukan mutane dubu 235,000 sakamakon yadda suke dauke da bayanai na yaki da abubuwa marasa dadin kallo.

A bayanan da shafin ya fitar a yanar gizo ya tunatar da cewa, a watan Fabrairu ya rufe shafukan mutane dubu 125,000.

Sanarwar ta ce, a yanzu kuma shafin ya dada hana mutane dubu 235,000 amfani da shi wanda hakan ya kai adadin zuwa dubu 360,000 a cikin shekara 1.

Kamfanin na Twitter ya ce, yana la’antar duk irin wadannan abubuwa kuma ya dauki matakin bayar da dukkan taimako wajen cire irin wadannan abubuwan na rikici daga shafukansa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.