Tafiyar Buhari wata makarkashiya ce -Inji PDP

Sanarwar da Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce PDP na sane da makarkashiyar da aka kitsa a wani taro ranar Laraba tsakanin fadar shugaban kasa da sanatoci ‘yan APC, na sake bude majalisa ala tilas tare da rakiyar jami’an tsaro da nufin tsige shugaban Majalisar dattijai Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

Shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari zai yi hutunsa ne a London daga ranar uku ga watan Augusta na shekarar 2018.

A wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta nuna cewa tuni Muhammadu Buhari ya aika da takarda zuwa ga shugaban Majalisar dattijai da kuma na majalisar wakilan kasar domin sanar da su game da hutun nasa.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne zai zama shugaban riko a lokacin da Buhari din zai yi hutun nasa a birnin London na kasar Burtaniya.

Wannan zargi da PDP din ke yi ya zo ne bayan da wasu daga cikin sanatoci, da suka hada har da shugaban Majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki suka sauya Sheka daga jam’iyyar APC wadda ke da rinjaye a majalisar, zuwa PDP, wadda ita ce ta biyu a yawan wakilan majalisar.

Tun bayan sauya shekara da Bukola Saraki ya yi, ana ta muhawara kan matsayin shugabancinsa a majalisar, a lokacin da jam’iyyun biyu ke jayayya kan wadda ta fi yawan wakilai a majalisar.

BBC HAUSA

Source: https://ift.tt/2Knk4aA

Leave A Reply

Your email address will not be published.