Tasirin Kudi Game Da Rayuwar Dan Adam A Kimiyyan Ce

Tasirin Kudi Game Da Rayuwar Dan Adam

A cikin wani littafin nazarin halayyar dan adam mai suna PSYCHOLOGY OF INTELLIGENCE ANALYSIS wanda RICHARD J. HEUER Jr. Ya rubuta cewar kudi Sam bashi da wani tasiri a bangaren chanjin halayya ta dan adam

Marubuchin yace shi kudi kawai yana fito da ainihin yadda halin dan adam yake ne wanda a baya talauchi ya boye

Misali kana iya samun mutum ainihin halayyar sa itace mugunta ko mugun hali irinsu wulakanchi girman kai nuna isa da sauransu amma saboda talauchi sai wannan halayyar tasa ta boye ya zama na koda yana da niyyar bayyana wannan halayyar tasa to ba zai iya ba domin karfin talauchi ya danne shi

Haka zalika ana iya samun mutum mai kyakkyawan hali kawaichi saukin kai kyauta fara’a barkwanchi da sauransu amma karfin talauchi ya saka ba zai iya nuna kyakkyawar halayyarba domin rashin iko

Shiyasa idan mutum ya samu kudi sai aka ga chanji chikin dabi’un sa to ba kudin ne suka chanza shi ba hakikannin dabi, ar sa ce yake bayyanawa walau halayyar kirki ko kuma ta banza

Rubutawa: Faruk Abdullahi Tukuntawa

Leave A Reply

Your email address will not be published.