Tesla Company : Zasu Kaddamar Da Sabuwar Mota Mai Amfani Da Haske

 Tesla Company

Shugaban kamfanin motoci na “Tesla” Mr. Elon Musk, ya bayyanar da cewar, kamfanin na yunkurin kaddamar da wata sabuwar babbar mota, mai amfani da wuta a watan Satunba.

Shugaban ya bayyanar da hakan ne a shafin shi,na Twitter, duk dai da bai bada cikakken bayani ba, ko motar zata zama mai tuka kanta ne ko wadda za’a dinga tukawane.

Haka kamfanin zasu kaddamar da jerin wasu motoci, masu daukar kaya daga nan zuwa watannin 18 zuwa 24. Yanzu haka dai kamfanin na siyar da motoci kirar Model S da Model X SUV, wanddanda suke amfani da wuta batare da shan feturba.

Kamfanin na cigaba da kokarin samar da wasu motoci masu rahusa, da basu amfani da fetur, suna amfani da hasken rana, ko kuma ayi cajin na motocin kamar yadda ake cajin wayar hannu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.