Ummi Zee Zee Ni Bana Karban Wa’azi Ko Nasihar ‘Yan Iska.

 Ummi Zee Zee 1

Ummi Zee Zee Ni Bana Karban Wa’azi Karya Ko Nasihar ‘Yan Iska.

Kamar yadda tsohuwar Jarumar ta rubuta a shafinta na Instagram, cikin sakonta na gargadi game da masu yi mata katsalandan a cikin harkokinta da yi mata nasiha.

Inda ta mayar musu da martanin cewa itafa bata karban wa’ azi karya ko Nasihar ‘yan Iska, sai dai idan kafin mutum yayi mata nasiha toya tabbatar cewa shima baya aikata kuskure.

Idan ko har yana aikatawa toya je ya fara gyara nashi tukunna kafin yazo yace zai yi mata wa’ azi karya ko nasiha.

Gadai Rubutun Da Jarumar Ta Wallafa Kamar Haka.

Duk mai son yamin wa’azin karya ko nasihar cin mutumci to ya tabbatar shima baya sabon allah kuma baya kuskure a rayuwarsa,in kuma har mutum ya tabbatar yana sabon allah kuma yana kuskure to ya fara gyara nashi rayuwar kafin yazo ya gyara nawa domin ni bana daukar hudubar dan iska sai hudubar mutum na gari nake dauka saboda manyan malamai magabata masu ilimi na addini sun yi dogon nazari sun gano duk wanda zaka ji yana zagin wani yana cewa wane ai dan iska ne ko baida tarbiya to sunce shima irin wanen da yake zagi ne dan salihin mutum baya zagin kowa.kuma haka annabi muhammad s.a.w yace in kaga mutum yana abubuwa marasa kyau to nasiha kadai aka umarce ka’ ka masa ba zagi ba ammah ina mamakin mutane’mu yan fim duk abunda mukayi abun zagi ne agun mutune sai kace sudin basa sabon allah ko kuskure.wasu wanda ba yan fim bama abunda sukeyi ko kare bazaici ba.ammah da yake shi dan fim shi aka sani to laifin sane abun maganah.  wasu mutanen na kula dabbobi ma sunfi su sanin ya kamata wallahi domin ko dabba baya aibata dabba dan uwansa, ammah sai kaga mutum yana aibata mutum dan uwansa tamkar shi yake da aljanna da zai bashi.sannan wani lokacin rashin aikinyi ne yake sa mutum ya ajiye rayuwarsa ya shiga na wani yana zaginsa bayan kai kanka abun zagi ne.sannan wani lokacin ma hassada ita take sa kayi ta zagin mutum ba abunda yama sai dan kawai ya fika ni’imar rayuwa .mtswwwww to LA’ILAFI QURESH’.

 Ummi Zee Zee

® www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.