Wani Dan Treda Ya Sama Karenshi Suna Buhari A Jihar Ogun

Kamar Yadda Jaridar Vanguard Ta Ruwaito Tace Matashin Mai Suna Chinakwe Ya Fadawa Abokansa Cewa Su Kashe Karen Nasa Su Kuma Cinyeshi Tun Biyo Bayan Da Hukumar ‘Yan Sandan Yankin Nasu Ta Kamashi Inda Matashin Ya Ce Ya Tsince Kanshi A Tsaka Mai Wuya.

Tun Biyo Bayan Aukuwar Lamarin Ne Dai Dubban ‘Yan Arewa Mazauna Yankin Suka Dauki Alwashin Cewa Indai Suka Ganshi Sai Sun Kasheshi Kuma Sun Cinye Namashi Danye.

Wani Dan Uwan Wannan Matashi Mai Suna Chiedozie Yace, Shidai Baiga Laifin Dan Uwan Nasaba, Inda Kuma Ya Kara Da Cewa Yana Tsoron Karda A Sama Dan Uwan Nasa Guba A Abinci Ko Kuma A Tsareshi A Gidan Kurkuku Har A Manta Dashi.

A Cewa Wata Majiya Ta Hukumar ‘Yan Sandan Yankin Tace Chinakwe Bawai Kawai Ya Kira Karensa Da Suna Buhari Bane A,a Har Rubutawa Yayi A Jikinsa Baro Baro Kowa Na Gani, Kuma Ya Rinka Yawo Da Karen Nasa A Unguwan nin Da ‘Yan Arewa Suke Da Zama Domin Tagalar Fada.

Abimbola Ovenemi Mai Rikon Mukamin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ta Ogun Ya Tabbatar Da Aukuwar Lamarin Tareda Kama Wannan Tantiri. Ya Kumace Yana Nan Yana Iya Bakin Kokarinsa Wajen Jin Ta Bakin Baturen Dan Sanda Na Sango Inda Abun Ya Faru Domin Samun Karin Bayani

Leave A Reply

Your email address will not be published.