Wani matashi ya hallaka kansa saboda budurwa ta yaudareshi

Matashi dan kasar Uganda ya hallaka kansa bayan yaji labarin budurwarsa tayi baikon aure da wani saurayi.

A wani rahoton jaridar PUNCHng ta wallafa Matashin mai suna Anthony Anyiza ya bar Uganda tun watan June, ya tafi Massachusetts domin yin hutu. Daga bisani sai akaji labarin gawarsa.

‘Yan sanda sun bayyana cewa “wata mata ce ta samu gawar matashin a wani kebabben wuri kuma ana zargin shine ya kashe kansa.

A bangare iyalan mamacin sun bayyana cewa basu zargin kowa akan wannan kisa sun barwa ‘yan sanda wuka da naman bincike akan lamarin.

Wasu membobin Cochin da mahaifin matashin yake jagoranta sun bayyana cewa  abinda sukeda tabbaci kawai shine sun san cewa zuciyarsa ta kadu yana cikin damuwa lokacinda aka sanar dashi budurwarsa zata kulla aure da wani.

An kuma bayyana cewa budurwar matashin ‘yar asalin America ce kuma ta bar kasar tun lokacinda ta fara shirye shirye sa dora hotunan biki a kafar sadarwa.

Source: https://ift.tt/2LNOp7R

Leave A Reply

Your email address will not be published.