Yadda Ta Musgunawa Kishiyar Ta Makauniya, Ya Zama Silar Ganinta

Yadda Ta Musgunawa Kishiyar Makauniya, Ya Zama Silar Warkewan ta

Yadda Ta Musgunawa Kishiyar Ta, Makauniya, Ya Zama Silar Ganinta.

Daga Mairo Muhammad Mudi

Aikata Alheri Ga Kowa

Ina yarinya, kakata ta ba ni wani labari wanda ya ke tasiri a rayuwata. Dafatan in kun karanta labarin zai yi tasiri a gare ku kuma. Allah Ya jikanta da rahama, amin.

Akwai wani magidanci yana zaune da uwargidansa ba su samu haihuwa ba sai ya yanke shawarar kara aure.

Da ya tashi aure, abin mamaki sai ya auro makauniya. Ita kuwa uwargida ta yi murnar haka don a ganinta wannan makauniyar ba za ta samu galaba a kanta sai abinda ta yi a tsakiyar gida kuma kila har ta yi ta gama, ita ma ba da haihu ba.

Suna zaune tare amma ta yi ta mata keta wanda ita makauniyar ba ta ma gani ba balle ta san an yi. Allah Ya taimaki makauniyar komai da kanta take, ga ta da tsabta, kullum a share-share ta ke duk da uwargidan kan bata mata in ta yi amma kuma za ta sake duk da cewa ba ta san an bata mata aikin da ta yi ba. Miji zai dawo ya ga gida tas, ruwan randa fes ga shi ta iya abinci.

Uwargidan za ta ce ita ta yi mata tunda ina za ta samu idon yi, miji sai ya yi godiya, ita kuwa makauniya ba ta san wainar da ake toyawa ba.

Allah cikin ikonSa sai ya bai wa makauniya ciki kuma ya ba ta cikin sauki, babu lolayi saboda haka uwargidan ba ta ankara ba sai da ciki ya yi girma.

Abin mamaki, ta yi murna tare da nuna farin cikin karuwa da za su samu. Ana nan, ana nan, makauniya ta haifi da namiji kyakkyawa son kowa, uwargidan ta ce kar a dauki wata mai mata hidima tunda ga ta, ita za ta yi mata komai, maigida ya amince tare da sa mata albarka.

Da aka kawo mata nama da za a dafa wa maijego da yaji sai ta karba ta yi miya amma kuma sai ta hana ta, ta dauko wata miyar daban da dama ta yi ta ba ta.

Ta ce mata,  “miyar hajji ce amma za ki ji su kanana, maigida kin san ba shi da kudi shiyasa ya sayo kanana.”

Makauniya ta karba ta yi godiya ta zauna ta hau shan miyar ita kuwa kishiyarta dadi kashe ta. Ashe ba miyar hajji ba ce, tana ta ce ta samo da dama ta zo ta yi mata miyar saboda da tsananin keta da kishi.

Makauniya tana shan miyar tana godiya, can ta je jan “hanji” sai miya ta yi tsalle zuwa fuskarta ta shiga mata ido. Sai ta ji zafin yaji, ta ce wa kishiyarta ta taimaka mata da ruwa, ta mika mata ruwa tana murmushi.

Wanke idonta ke ta wuya sai idanuwa suka bude sai ta ga abinda ta ke ci gabanta, ta yi tsalle ta koma da baya tana ce mata, “ashe maganin makanta kika ba ni, ashe tana na maganin makanta.”

Nan da nan gida ya cika kowa yana, Allah wadai da irin halinta sannan aka yi ta taya makauniya murna bibbiyu, ga ta haihuwa ga ta samun ido.

Darasi-Hasada da keta ba su tasiri ga wanda Allah Ya yi nufin daukakawa saboda haka babu amfani gabatar da su don ba za su yi tasiri ga rayuwar wanda kake son cutawar ba saboda Allah Shi ke da ikon zartar da hukuncinSa ga bayinSa ba wani ba.

2. In har ka ga hasada ta yi tasiri, to ka san jarabawa ce Allah Ya daura ka a kai bisa dalilai biyu, Ya baka nasara ya ga iya yinka akan bawanSa don in Ya tashi kama ka babu wajen buya ko kuma Allah na baka damar ka tuba ne ka dawo hanya ta gari don Shi mai yawan gafara ne saboda haka duk wanda ke kulla wa wani abinda ya san bai dace ba ya yi maza ya daina kana ya tuba.

3. Kar ka rena kowa ko walakanta wani saboda ba ka san irin baiwar da Ya yi masa ba haka nan mu san cewa ba mu da wani dalilin da za mu rike mu ce, Allah ba zai jarabce mu kamar wanda ya ke cikin jarabawarSa har kake walakantawa ba.

Allah Ya sa mu gane, Ya kuma sa mu fi karfin zukatanmu.

©Zuma Times Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.