Yadda ‘yan Boko-Haram suka kashe min yaro na dan shekara uku a madadi na.

Yadda yan Boko-Haram suka kashe min yaro na dan shekara uku a madadi na.

Daga : Muhammad Ismail Ali.

Na ziyar ci gidan wani malami a garin na Damboa sai na taradda wani bawan Allah dan garin mulgai kuma dama yasan ni bayan mun gaisa dashi sai na tambaye shi? Ina Muktar danka yanzu dai ya girma ko? Dan dama nasan yaron sai yace ai yan Boko-Haram sun kashe shi nace Inna lillahi Muktar din? Yace eh nace ya hakan ya faru? Sai yace, “sun kawo hari anan Damboa sai suka samu dama har sun shiga cikin gari suka fada a unguwar mu sai mu maza muka gudu muka bar iyalan mu to suna shiga cikin unguwar mu basu tsaya sai a gidana suna shiga suka tambayi matata ina nake tace bana nan sun neme mi a cikin gidan basu same ni ba sai kawai suka CE ma matata ta mika musu yaron dake hannun ta ko su harbe ta tana mika musu shi sai daya yace ku harbe shi a madadin baban sa idan ya girmama ba abunda zaiyi sai kafirci kamar yanda uban shi ya kafirce sai suka harbi yaron da bai d’ara shekara uku ba, kuma suka ce ma matata kicewa mijin ki mun kashe dansa idan ya isa yabi bayan mu ya dauki fansan dansa idan ya isa sai sukayi tafiyar su yace min “Kan zuciyar Muktar suka harba har bilet ya fita ya huje Randar mu ma.
Yace akan hakane ma yanzu na shiga sahun yan banga sai na dau fansan dana.

To yan uwana kunji yanda yan Boko-Haaram suka aiwatar da kisa akan wannan yaro dan shekara 3 uku wai da sunan laifin mahaifinsa wai ko daga baya zai zo ya kafirce kamar yanda baban sa ya kafirce.

Ya Allah ka karya duk wanda yake da hannu wajen kashe mu ka dai-dai tashi tun nan duniya ya Allah.

® Muhammad Ismail Ali.
6-5-2017.

Leave A Reply

Your email address will not be published.