Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Sama Sun Cafke ‘Yan Bindiga 16 A Jihar Zamfara

Rundunar Sojin sama ta 207 da aka jibge a garin Gusau na jihar Zamfara, ta sanar da cafke ‘yan bindiga dadi guda 16 yayin da ta ke aikin kakkabe ‘yan ta’adda daga jihar mai taken ‘Operation Sharar Daji.

Shugaban dakarun Group Captain Caleb Olayera ya bayyana haka, yayin da ya karbi bakuncin babban hafsan Sojin sama Saddique Abubakar a ziyarar gani da ido da ya kai a garin Gusau.

Air Mashal Saddiq Abubakar, ya sanar da tura karin kayan aiki da su ka hada jiragen yaki da motoci zuwa jihar Zamfara daga sassan Nijeriya, domin tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’ummomin da ke jihar Zamfara.

Caleb, ya ce su na gudanar da samame ta sama, da kuma yawon sintiri da na leken asiri a cikin jirgin sama, kuma a dalilin haka sun kama wani kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi, wanda tuni sun mika shi ga hukumar yaki da sha da tu’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA.

Ya ce sun kwato bindigogi uku, da alburusai da dama daga hannun ‘yan bindigar, sa’annan sun kama ‘yan bindiga 16, yayin da su ka ceto mutane 8 da aka yi garkuwa da su, kuma biyar daga cikin su ‘yan sanda ne.

Source: Alummata.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.