Yan Lawadi : An Kashe Yan Luwadi 50 A Mashaya A Kasar Amurka

“Yan uwan wadanda abin ya ritsa da su na cikin tashin hankali

Magajin garin Orlando da ke Florida ta Amurka, ya ce zuwa yanzu mutane 50 ne suka mutu sakamakon wani bude wuta da wani dan bindiga ya yi a mashayar masu auren jinsi daya.

Wannan dai shi ne harin bindiga mafi muni da aka taba kai wa Amurka a tarihin kasar.

Wasu mutane 53 din kuma sun jikkata, suna kuma karbar taimakon gaggawa a asibiti.

Dukda Cewa Jami’an tsaro sun kai agajin gaggawa

Kafofin yada labaran Amurka sun gano mutumin da ya bude wutar a matsayin dan Amurka mai suna Omar Mateen.

Matashin mai shekara 29 yana dauke ne da babbar bindiga da kuma karama ta hannu a lokacin da ya bude wutar.

Ya yi garkuwa da mutane kusan 30 kafin daga bisani ‘yan sanda suka harbeshi har lahira.

Leave A Reply

Your email address will not be published.