‘Yan Nigeria mazauna Ghana na zaman dar-dar

Wasu ‘yan Nigeria mazauna Ghana sun koka bisa zaman dar dar da suke sakamakon wasu matasa da suke kawo musu hari a wuraren kasuwancinsu. 

‘Yan Nigeria wadanda suka ce ana nuna musu wariya a kasar ganin yadda ake muzguna musu kuma ba’daukar matakin gaggawa. 
Sun kara da cewa ” Wasu matasa na zuwa bakin shugunansu suna musu barazanar tashi tunda su baki ne ba yan kasa ba in kuna suka bijire sai su hau barnata musu kayan sana’arsu. 
Kungiyar ‘yan Nigeria masu gudanarda Sana’a a Ghana suma sun tabbatarda faruwar lamarin inda suka ce ana barazana ga membobinsu. Charman na kungiyar ya bayyana rashin jindadinsa game da lamarin. 
Saidai hukumar yan sanda a kasar tace  suna kokari wajen kare hakkunan bakin saidai matasan suna shammatarsu ne amma nan bada jimawa ba zasu dalike aukuwar lamarin. 
‘Yan sanda sun kara da cewa yanzu haka sun aika da Jami’ansu a yankin KUMASI domin kula ta musamman ga wurarenda abin ya shafa.

Source: https://ift.tt/2OxCs49

Leave A Reply

Your email address will not be published.