‘Yan uwan juna suna neman kujera daya a zaben daura

                                         Kabir Babba Kaita         Ahmad Babba kaita                                     

Kabir wan Ahmad ne domin mahaifinsu daya ne.

Ahmad shi ne dan majalisar mai wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada a majalisar wakilan Najeriya.

Shi kuwa Kabir tsohon ma’aikacin hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ne wato kwastam.

Dukkansu ‘ya’yan mutum dayane kuma suna neman kujera daya wacce marigayi senata Mustapha Bukar ya rasu ya barta.

Duk wanda yasamu nasarar lashe zaben cike gurbin shine zai zama wakilin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zaa wakilci mahaifarsa Daura dake Katsina ta arewa.

‘Yan uwan ‘yan takarar Hajiya Rabi Babba kaita da Ali Babba Kaita sun shaida cewa babu wata gaba ko rashin jituwa tsakanin mutanen biyu kuma suna ganin wannan wani cigaba ne a demokradiyya ace ‘yan uwa biyu sun nemi kujera kuma babu rashin jituwa tsakaninsu.

‘Yan uwan sun kuma ce dukkan mutanen biyu suna martaba juna kuma shi Ahmad ya dauki Kabir Babban wa uba ne.

Saidai masu sharhi da tofa albarkacin baki suna kan tofawa kan lamarin don ganin ya zata kaya a tsakanin ‘yan uwan juna kuma masu neman kujera daya.

Source: https://ift.tt/2vwma3B

Leave A Reply

Your email address will not be published.