Yanzu Haka Hukumomi Biyu Ne Ke Binciken Sarkin Kano Karanta Kuji

Yanzu Hukumomi Biyu Ne Ke Binciken Sarkin Kano

Salihu Garba Daga Rahoton VOA

Binciken da majalisar dokokin Kano ta kaddamar jiya kan masarautar Kano kari ne akan wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ko EFCC reshen Kano ta ke yi bisa zargin barna da dukiyar jama’a da aka ce masarautar ta yi tun daga lokacin da sarki mai ci yanzu ya hau karagar mulki.

Baicin zargin da ake yi masa da yin watanda da kudade ana kuma zarginsa da shiga harkokin siyasa da aiwatar da wasu ayyuka da suka ci karo da al’adun fada wadanda suke cikin zargin da majalisar dokokin jihar ta yi wa sarkin.

To amma Malam Ibrahim Ado Kurawa masanin tarihi da ayyuka da ka’idojin fadar Kano na cewa a matsayin Sarki Muhammada Sanusi ll na masanin tattalin arziki duk duniya na gayyatarsa ya gaya masu yadda za su gyara abubuwa. Shin idan an neme shi ya taimaka da gyara sai ya ki?

Ya ce, mutanen Arewa suna ba shi mamaki. Lokacin da ake rigingimu an soki sarakunan da rashin cewa komi. Yanzun Sarki Sanusi yana fadan abubuwan da aka yi ba daidai ba an ce ya yi laifi.

Yana mai cewa Sarki shi ne fada. Duk abun da ya ga dama zai yi shi. Abu daya ne ba zai yi ba shi ne ya yi wa Allah sabo. Ya ce sabo da haka mutane su daina cewa sarki ya sabawa abun da ake yi a fada.

Yanzu dai hukumomi guda biyu ne ke gudanar da bincike akan aikata ba daidai ba da ake zargin Sarkin Kano da yi.

Barrister Audu Bulama Bukarti na tsangayar aikin lauyoyi da ke Jami’ar Bayero ta Kano ya yi tsokaci ta fuskar shari’a.

Ya ce dokar kasa ta ba hukumomin da ke binciken sarkin su bincike shi idan har an yi wani abu da ba daidai ba musamman wajen kashe kudaden al’umma. Sai dai ya ce abun duba shi ne yaya za’a ce hukumomi biyu na bincike akan abu daya.

Ya ce dokar da ta kafa EFCC ba za ta bari ta ci gaba da binciken ba domin wata hukuma ta shigo. Kwamitin binciken majalisar dokoki na ‘yan siyasa ne kuma babu yadda ba za’a shigo da batun siyasa ciki ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.