Za A Fara Karbar Haraji Daga Masu Buga Wayar Salula A Nigeria

Za A Fara Karbar Haraji Daga Masu Buga Wayar Salula A Nijeriya

Gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emiefele ya baiwa gwamnati shawarar duba yiwuwar fara karbar haraji daga masu buga wayar salula da ya haura mintuna uku, domin samun kudin shiga.

Gwamnan babban bankin ya ce idan aka samu nasarar kaddamar da hakan kasar zata samu kudin shiga kimanin Naira Biliyan Dubu 100 a shekara.

Sai dai yace wannan mataki ba zai shafi masu karamin karfi ba, domin kuwa za a rika cajar harajin ne daga wadanda suka buga wayar da ta haura minti uku kacal, wanda kuma yace dawuya a samu talakan dake buga waya sama da mintuna uku.

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya zanta da wasu ‘yan Nijeriya a jihar Lagos, yayin da wasu ke ganin yin hakan ba zai takura ba, wasu kuwa na ganin wannan wata hanyar zalunci ce ga talaka domin akwai hanyoyi masu yawa da yakamata gwamnati ta mayar da hankali akai maimakon ta dinga cirar wannan haraji…

Leave A Reply

Your email address will not be published.