Zaa Kaddamar Da Yaki Kan Tsagerun Niger Delta Idan Ba A Yi Sulhu Ba

Za A Kaddamar Da Yaki Kan Tsagerun Niger Delta Idan Ba A Yi Sulhu Ba

Ma’aikatar tsaro ta tabbatar da cewa da zarar aka kasa cimma wata yarjejeniyar sulhu da kungiyoyin tsagerun Niger Delta, za a kaddamar da gagarumin yaki a kan mayakan kungiyoyin wadanda a halin yanzu ke kai hare hare a bututun mai da ke yankin.

Wannan mataki na rundunar sojan ya biyo bayan gargadin Shugaban Kamfanin Mai na Kasa(NNPC) Dr. Maikanti Baru wanda ya nuna cewa idan har ba a dauki matakin gaggawa kan tsagerun ba,to kasar nan za ta shiga cikin rudani na rashin aiwatar da kasafin kudin bana.

Haka ma, kungiyar kare muradun yankin Niger Delta ta MEND ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin da nufin kawo karshen rikicin

Leave A Reply

Your email address will not be published.